1 Chronicles 7:40 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dukan waɗannan zuriyar Asher ne, kawunan iyalai, zaɓaɓɓun mutane, jarumawa sosai da kuma fitattun shugabanni. Yawan mutanen da suke a shirye don yaƙi, kamar yadda aka lissafta zuriyarsu, 26,000 ne.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكَنْ وَطَنَّنْ یَیَنْ ذُرِيَرْ أَشٜىٰرْ نٜىٰ؞ سُنْ ذَمَ شُوغَبَنِّنْ غِدَاجٜىٰنْ كَاكَنِّنْسُ دَ ڠُونَيٜىٰنْ يَاڧِ دَ مَنْيَ ثِكِنْ شُوغَبَنِّ؞ بِسَغَ تَارِيحِنْ أَصَلِنْ غِدَاجٜىٰنْ كَاكَنِّنْسُ سُنَدَ مَظَا دُبُو عَشِرِنْ دَ شِدَ وَطَنْدَ سُكَ إِسَ يَاڧِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗannan duka su ne zuriyar Ashiru, su ne kuma shugabannin gidajen kakanninsu. Zaɓaɓɓun jarumawa ne su, manyan sarakuni. Yawansu da aka lasafta bisa ga asalinsu don yaƙi su dubu ashirin da dubu shida ne (26,000).