1 Corinthians 1:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ina roƙonku ’yan’uwa, a cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, dukanku ku yarda da juna, domin kada a sami tsattsaguwa a cikinku, domin kuma ku zama ɗaya, cikakku a cikin halinku da tunaninku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنَ ضُواْڧُوانْكُ، یَنْعُوَ، سَبُواْدَ سُونَنْ عُبَنْغِجِنْمُ عِيسَىٰ أَلْمَسِيحُ ثٜىٰوَ بَرِ بَاكِنْكُ يَذَمَ طَيَ؞ كَدَ كُذَوْنَ أَرَبٜىٰ، سَيْدَيْ كُهَطَكَيْ، كُذَوْنَ دَ نُڢِ طَيَ، تُنَانِنْكُ كُمَ طَيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na roƙe ku 'yan'uwa, saboda sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, cewa dukanku bakinku yă zama ɗaya, kada wata tsaguwa ta shiga a tsakaninku, sai dai ku haɗa kai, kuna da nufi ɗaya, ra'ayinku ɗaya.