1 Corinthians 14:26 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Me za mu ce ke nan ’yan’uwa? Sa’ad da kuka taru, wani yakan yi waƙa, wani koyarwa, wani wahayi, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Dole ne a yi duka don gina ikkilisiya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تُواْ، يَيَ ذَاعَيِ كٜىٰنَنْ یَنْعُوَ؟ سَعَدَّ كُكَ تَارُ، وَنِ يَنَدَ وَاڧَرْ يَبُوانْ اللَّهْ ، وَنِ دَ كُواْيَرْوَا، وَنِ دَ بَيَانِ، وَنِ دَ يِنْ مَغَنَ دَ وَنِ هَرْشٜىٰ، وَنِ كُمَ دَ ڢَسَّرَ؞ بَرِ عَيِ كُواْمٜىٰ دُواْمِنْ غِنَاوَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
To, ƙaƙa abin yake ne, 'yan'uwa? Duk sa'ad da kuka taru, wani yakan yi waƙar yabon Allah, wani kuma koyar da Maganar Allah, wani bayani, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Sai dai a yi kome don ingantawa.