1 Corinthians 3:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na ba ku madara ba abinci mai tauri ba, domin ba ku balaga ba a lokacin. Kai, har yanzu ma, ba ku balaga ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَثِيَرْ دَكُو دَ مَدَرَ، بَ دَ عَبِنْثِ مَيْ تَوْرِ بَ، دُوانْ بَكُ إِسَ ثِنْ عَبِنْثِ مَيْ تَوْرِبَ؞ حَرْ يَنْذُ مَا بَكُ إِسَ بَ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Nono ne na shayar da ku, ba abinci mai tauri na ba ku ba, don ba ku isa ci ba a lokacin, ko a yanzu ma ba ku isa ba,