1 Corinthians 5:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yanzu dai ina rubuta muku cewa kada ku haɗa kai da duk mai kiran kansa ɗan’uwa, amma yana fasikanci, ko kwaɗayi, ko bautar gumaka, ko ɓata suna, ko mashayi, ko mazambaci. Kada ku ko ci abinci da irin wannan mutum.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا إِنَ رُبُوتَ مُكُ ثٜىٰوَ كَدَ كُهَطَكَيْ دَ دُكْ وَنْدَ عَكٜىٰ ثٜىٰ دَشِ طَنْعُوَ مَيْبِے عِدَنْ شِے مَيْ لَلَتَ نٜىٰ، كُواْ مَيْ ݣُوطَيِ نٜىٰ، كُواْ مَيْ بَوْتَرْ غُمَكَ، كُواْ مَيْ ذَاغٜىٰ ذَاغٜىٰ، كُواْ مَيْ بُغُوَ، كُواْ مَيْسَاتَا، كَدَكُ كُواْ ثِ عَبِنْثِ تَرٜىٰدَ إِرِنْ وَطَنَّنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai dai na rubuta muku ne, don kada ku yi cuɗanya da duk wanda ake kira ɗan'uwa, mai bi, in yana fasikanci, ko makwaɗaici, ko matsafi, ko mai zage-zage, ko mashayi, ko mazambaci, kada ku ko ci abinci da irin waɗannan.