1 Corinthians 7:34 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
hankalinsa a rabe yake. Mace marar aure ko kuwa budurwa ta damu ne da al’amuran Ubangiji. Nufinta shi ne ta ba da kanta ga Ubangiji cikin jiki da ruhu. Amma mace da take da aure ta damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda za tă gamshi mijinta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حَنْكَلِنْسَ يَرَبُ بِيُ كٜىٰنَنْ؞ كُمَ مَثٜىٰ مَرَرْ عَوْرٜىٰ، كُواْ يَارِنْيَ، تَكَنْ دَامُ دَ شَعَنِنْ عُبَنْغِجِ سُواْسَيْ يَدَّ ذَاتَ ذَمَ مَيْ ڟَرْكِے عَثِكِنْ جِكِے دَ رُوحُ؞ مَثٜىٰ مَيْ عَوْرٜىٰ كُوَ تَكَنْ دَامُ دَ أَبُبُوَنْ دُونِيَا، يَدَّ ذَاتَسَا مِجِنْتَ يَجِ دَاطِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Hankalinsa ya rabu biyu ke nan. Mace marar aure, ko budurwa, takan tsananta kula da sha'anin Ubangiji, yadda za ta kasance tsattsarka a jiki, da kuma a rai. Mace mai aure kuwa takan tsananta kula da sha'anin duniya, yadda za ta faranta wa mijinta rai.