1 Corinthians 7:35 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na faɗa haka don amfaninku ne, ba don in ƙuntata muku ba. Sai dai don ku yi rayuwa a hanyar da ta dace da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَڢَطِ حَكَ دُوانْ أَمْڢَانِنْكُنٜىٰ، بَ دُوانْ إِنْ مَاڟَ مُكُبَ، سَيْدَيْ دُوانْ ذَمَنْكُ يَيِݣَوْ، دُوانْ كُبَوْتَا وَ عُبَنْغِجِ بَاتَرٜىٰدَ رَبَ حَنْكَلِنْكُبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na faɗi haka ne, don in taimake ku, ba don in ƙuntata muku ba, sai dai don in kyautata zamanku, da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba.