1 Corinthians 7:36 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In mutum ya ga cewa ba ya nuna halin da ya kamata ga budurwar da ya yi alkawarin aure da ita, in kuma shekarunta suna wucewa, shi kuma ya ga ya kamata yă yi aure, to, sai yă yi. Ba zunubi ba ne. Ya kamata su yi aure.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا عَثٜىٰ مُتُمْ يَيِ أَلْڧَوَرِ دَ وَتَ دَ تَ إِسَ عَوْرٜىٰ، كُمَ يَنَ ڟَمَّنِ يَنَ يِنْ أَبِنْدَ بَيْ دَاثٜىٰبَ غَرٜىٰتَ، سَعَنً يَنَ شَعَوَرْتَ سُواْسَيْ، سَيْ يَ عَوْرٜىٰتَ؞ عِدَنْ حَكَنٜىٰ، بَ لَيْڢِے بَنٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga zancen 'ya budurwa, wadda ta zarce lokacin aure, idan mahaifinta ya ga bai kyauta mata ba, in kuwa hali ya yi, sai yă yi abin da ya nufa, wato, a yi mata aure, bai yi zunubi ba.