1 Corinthians 9:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In waɗansu suna samun wannan taimako daga gare ku, ashe, mu ba mu fi cancanta mu samu ba? Amma ba mu yi amfani da wannan ’yancin ba. A maimakon haka, mun jure da kome, domin kada mu hana bisharar Kiristi yaɗuwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حَرْ عِدَنْ وَطَنْسُ سُنَدَ دَامَرْ يِنْ حَكَ، أَشٜىٰ، بَمُڢِسُ دَامَرْ يِنْ حَكَبَ؟ دُكْدَهَكَ، بَمُيِ أَمْڢَانِ دَ وَنَّنْ دَامَرْ بَ، عَمَّا مُنْ جِمْرٜىٰ دَكُواْمٜىٰ أَمَيْمَكُوانْ كَٰوُاْ أَبِنْدَ ذَيْ حَنَ عَيْكِنْ لَابَرِ مَيْ دَاطِے نَ أَلْمَسِيحُ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da yake waɗansu sun mori halaliyarsu a game da ku, ashe ba mu muka fi cancanta ba? Duk da haka ba mu mori wannan halaliya ba, sai dai muna jure wa kome, don ta koƙaƙa kada mu hana bisharar Almasihu yaɗuwa.