1 John 5:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kowa ya gaskata cewa Yesu shi ne Kiristi, shi haifaffe na Allah ne, kuma duk mai ƙaunar mahaifi kuwa, yakan ƙaunaci ɗansa ma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ وَنْدَ يَبَادَ غَسْكِيَ ثٜىٰوَ عِيسَىٰ نٜىٰ أَلْمَسِيحُ ، مُتُمِنَّنْ طَنْ اللَّهْ نٜىٰ؞ دُكْ مَيْ ڧَوْنَرْ عُبَنْ ذَيْ ڧَوْنَثِ طَنْ مَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kowa da yake gaskata Yesu shi ne Almasihu, haifaffen Allah ne. Kowa yake ƙaunar mahaifi kuwa, yana ƙaunar ɗa kuma.