1 Kings 1:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ta ce masa, “Ranka yă daɗe, kai kanka ka rantse mini ni baiwarka da sunan Ubangiji Allahnka cewa, ‘Solomon ɗanka zai zama sarki bayana, zai kuma zauna a kujerar sarautata.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَا أَمْسَ تَثٜىٰ «رَنْكَيَدَطٜىٰ، سَرْكِے! كَارِغَا كَا ضَنْڟٜىٰ مِنِ دَ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكَ ثٜىٰوَ سُلَيْمَٰنُ طَانَ نٜىٰ ذَيْ يِمُلْكِ بَايَنْكَ، ذَيْ كُوَ ذَوْنَ عَكُجٜىٰرَرْ مُلْكِنْكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ta ce masa, “Ranka ya daɗe, ka riga ka rantse mini da sunan Ubangiji Allahnka, ka ce, ‘Sulemanu ɗanki zai yi mulki bayana, shi ne zai hau gadon sarautata.’