1 Kings 1:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya miƙa hadayun shanu, da shanun da ake kiwo a gida, da tumaki masu yawa, ya kuma gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza, da Abiyatar firist, da Yowab shugaban mayaƙa, amma bai gayyaci Solomon bawanka ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَرِغَا يَمِيڧَ هَدَايَرْ شَانُو دَ دَبُّواْبِنْ دَ عَكَيِ كِيوُانْسُ أَغِدَا دَ تُمَكِ مَاسُيَوَ؞ يَغَيَّثِ أَبِيَتَرْ ڢِرِسْتِ دَ يُواْوَبْ شُوغَبَنْ سُواْجُواْجِنْكَ، تَرٜىٰدَ دُكَنْ یَیَ مَذَنْ سَرْكِے، عَمَّا بَيْ غَيَّثِ مَيْ حِدِمَرْكَ سُلَيْمَٰنُ بَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya miƙa hadaya da bijimai, da turkakkun dabbobi, da tumaki da yawa. Ya kuma gayyaci dukan 'ya'yan sarki, da Abiyata firist, da Yowab shugaban sojoji, amma bai gayyaci Sulemanu ɗanka ba.