1 Kings 1:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka bayinsa suka ce masa, “Bari mu nemi wata budurwa wadda za tă yi wa ranka yă daɗe, sarki hidima, tă kuma kula da shi. Za tă dinga kwanta kusa da ranka yă daɗe, yă ji ɗumi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مَاسُ يِمَسَ حِدِمَ سُكَثٜىٰ «رَنْكَيَدَطٜىٰ، بَرِ مُنٜىٰمُواْ مَكَ يَارِنْيَرْ دَ ذَاتَ ذَوْنَ تَرٜىٰدَكَيْ تَلُورَ دَكَيْ؞ ذَاتَ دِنْ‌غَ ݣُونْتَ أَغٜىٰڢٜىٰنْكَ دُوانْ تَسَا كَجِ طُمِ، يَا مَيْغِرْمَ سَرْكِے؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saboda haka fādawansa suka ce masa, “Ranka ya daɗe bari mu nemo maka budurwa, wadda za ta zauna tare da kai, ta riƙa yin maka hidima, ta kwanta a ƙirjinka don ka riƙa jin ɗumi.”