1 Kings 1:41 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Adoniya tare da dukan baƙin da suke tare da shi kuwa suka ji wannan sa’ad da suke gama bikinsu. Da jin busan ƙaho, sai Yowab ya yi tambaya, ya ce, “Me ya jawo surutu haka a birni?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَدُواْنِيَ تَرٜىٰدَ دُكَنْ بَڧِنْ دَسُكٜىٰ دَشِ سُكَجِ إِيهٌ دَيْدَيْ سُنَ ڧَارٜىٰ بِكِنْسُ؞ دَ يُواْوَبْ يَجِ بُوسَرْ ڧَهُواْ سَيْيَثٜىٰ «مٜىٰ يَجَٰوُاْ إِيهُ عَثِكِنْ بِرْنِ حَكَ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Adonija da dukan baƙin da suke tare da shi suka ji amon sowa bayan da suka gama cin abinci. Da Yowab ya ji busar ƙaho, sai ya ce, “Mene ne dalilin wannan hargitsi a birni?”