1 Kings 1:42 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Tun yana cikin magana, sai Yonatan ɗan Abiyatar ya iso. Adoniya ya ce, “Shigo! Ai, mutumin kirki irinka, lalle ka kawo labari mai daɗi ne.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يُواْوَبْ يَنَ ثِكِنْ مَغَنَ كٜىٰنَنْ، سَيْغَاشِ يُواْنَتَنْ طَنْ أَبِيَتَرْ ڢِرِسْتِ يَ إِسُواْ وُرِنْ؞ سَيْ أَدُواْنِيَ يَثٜىٰ مَسَ «شِغُواْ، غَمَا كَيْ مُتُمِنْ كِرْكِنٜىٰ، لَلَّيْ كَنَ كَٰوُاْ لَابَرِ مَيْ دَاطِے؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yana cikin magana ke nan sai ga Jonatan ɗan Abiyata, firist, ya zo. Adonija ya ce musu, “Shigo, gama kai nagarin mutum ne, ka kawo albishir.”