1 Kings 1:51 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da aka faɗa wa Solomon cewa, “Adoniya yana tsoron Sarki Solomon, kuma ya manne wa ƙahonin bagade. Yana cewa, ‘Bari Sarki Solomon yă rantse mini a yau cewa ba zai kashe bawansa da takobi ba.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكَ ڢَطَا وَ سُلَيْمَٰنُ ثٜىٰوَ أَدُواْنِيَ يَنَ جِنْ ڟُواْرُوانْسَ؞ غَاشِ يَكَامَ ڧَهُواْنِنْ بَغَدٜىٰ يَنَ ثٜىٰوَ «بَرِ سَرْكِے سُلَيْمَٰنُ يَرَنْڟٜىٰ مِنِ ثٜىٰوَ بَذَيْ كَشٜىٰنِبَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Aka faɗa wa Sulemanu cewa ga Adonija yana jin tsoron sarki Sulemanu, gama, ga shi, ya kama zankayen bagade, yana cewa, “Bari sarki Sulemanu ya rantse mini tukuna, cewa ba zai kashe ni ba.”