1 Kings 1:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wata rana Adoniya ya tafi Dutsen Zohelet kusa da En Rogel, inda ya yi hadayar tumaki, da shanun noma, da shanun da ake kiwo a gida. Ya kuma gayyaci ’yan’uwansa, wato, sauran ’ya’yan Sarki Dawuda, tare da dukan dattawan sarki da suka fito daga Yahuda,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَتَرَانَ أَدُواْنِيَ يَتَڢِے دُوڟٜىٰنْ ذُواْهٜىٰلٜىٰتْ كُسَدَ عٜىٰنْرُواْغٜىٰلْ، عِنْدَ يَيِ هَدَايَرْ تُمَكِ دَ شَانُنْ نُواْمَ دَ شَانُنْ دَ عَكٜىٰكِيوُاْ أَغِدَا؞ يَكُمَ غَيَّثِ یَنْعُوَنْسَ، وَتُواْ سَوْرَنْ یَیَنْ سَرْكِے دَاوُدَ، تَرٜىٰدَ دُكَنْ دَتَّاوَنْ سَرْكِے دَ سُكَ ڢِتُواْ دَغَ يَهُودَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Adonija kuwa ya yi hadaya da tumaki, da bijimai, da turkakkun dabbobi kusa da Dutsen Zohelet, wato dutsen maciji, wanda yake gab da Enrogel. Ya gayyaci dukan 'yan'uwansa, 'ya'yan sarki, da fādawan da suke a Yahuza.