1 Kings 10:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kujera sarautar ta kasance da matakai shida, kuma bayanta tana da bisa mai kamannin gammo. A kowane gefen kujerar akwai wurin sa hannu, da kuma zaki tsaye kusa da kowannensu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُجٜىٰرَرْ مُلْكٍ تَنَدَ مَتَاكَيْ شِدَ؞ كَنْ كُجٜىٰرَرْ نَوُرِنْ سَا بَايَ، أَنْسَسَّڧَ كَمَرْ بَكَنْ دَ عَكَ لَنْڨُوسَ؞ عَكُواْوَنٜىٰ غٜىٰڢٜىٰ نَكُجٜىٰرَرْ أَݣَويْ وُرِنْ أَجِيٜىٰ حَنُّ؞ أَݣَويْ صِڢَّرْ ذَاكِ أَڟَيٜىٰ كُسَدَ كُواْوَنٜىٰ وُرِنْ أَجِيٜىٰ حَنُّنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gadon sarautar yana da matakai shida da siffar kan maraƙi a bayan gadon sarautar, a kowane gefen mazaunin kuma, akwai wurin ɗora hannu da siffofin zaki biyu suna tsaye a gefen wuraren ɗora hannun.