1 Kings 10:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki yana da jerin jiragen ruwan kasuwanci a teku, tare da jiragen ruwan Hiram. Sau ɗaya kowace shekara uku jerin jiragen yakan dawo ɗauke da zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da birai marasa wutsiya, da kuma gogon biri.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا سَرْكِے يَنَدَ جِضَاغٜىٰنْ ضُوَ نَكَاسُوَنْثِ مَاسُبِنْ تٜىٰكُ تَرٜىٰدَ جِضَاغٜىٰنْ ضُوَ نَ حِرَمْ؞ كُواْوَثٜىٰ شٜىٰكَرَا عُكُ، جِضَاغٜىٰنْ سُكَنْ دَاوُاْ دَ ظِينَارِيَ دَ أَظُرْڢَا دَ هَڧُواْرِنْ غِيوَ دَ مَنْيَنْ بِرَيْ دَ تَلُواْتَلُواْ مَاسُ أَدُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama sarki yana da rundunar jiragen ruwa a tekun Tarshish tare da na Hiram. Sau ɗaya a shekara uku rundunar jiragen ruwa na Tarshish sukan kawo zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da birai, da ɗawusu masu daraja.