1 Kings 10:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kowace shekara, kowa da ya zo wurinsa yakan kawo kyautai, kayayyakin azurfa da na zinariya, riguna, makamai, da kayan yaji, dawakai da alfadarai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْوَنّٜىٰنْسُ يَكَٰوُاْ ݣَوْتَرْسَ تَكَايَنْ أَظُرْڢَا دَ نَظِنَرِيَ دَ رِيغُنَ دَ كَايَنْ يَاڧِ دَ كَايَنْ يَجِ دَ دَوَكِ دَ جَاكُنَنْ دُواْكِ؞ وَنَّنْ يَثِيغَبَ كُواْوَثٜىٰ شٜىٰكَرَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kowannensu yakan kawo masa yawan kyautai na kayayyakin azurfa, da na zinariya, da riguna, da turare, da kayan yaji, da dawakai, da alfadarai kowace shekara.