1 Kings 10:26 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Solomon ya tara kekunan yaƙi da dawakai; ya kasance da kekunan yaƙi dubu goma sha huɗu, da dawakai dubu goma sha biyu waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi, ya kuma ajiye tare da shi a Urushalima.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُلَيْمَٰنُ يَتَتَّارَ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْ يَاڧِ دَ دَوَكِ؞ يَنَ دَ كٜىٰكُنَنْ يَاڧِ دُبُو طَيَ دَ طَرِے حُطُ دَ دَوَكِنْ يَاڧِ دُبُو غُواْمَشَا بِيُ؞ يَكَڢَسُ أَغَرُضُوً أَجِيَرْ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْ يَاڧِ دَ كُمَ عِنْدَ سَرْكِے يَكٜىٰدَ ذَمَ، وَتُواْ عُرُوشَلِيمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sulemanu kuwa ya tattara karusai da mahayan dawakai. Yana da karusai dubu da ɗari huɗu (1,400), da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000), waɗanda ya zaunar da su a biranen karusai da kuma waɗansu tare da shi a Urushalima.