1 Kings 10:29 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka yi jigilar kekunan yaƙi daga Masar a bakin shekel ɗari shida na azurfa, doki ɗaya kuma a kan ɗari da hamsin. Sun kuma yi jigilarsu suna sayarwa ga dukan sarakunan Hittiyawa da na Arameyawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَ عِيَ كَٰوُاْ كٜىٰكٜىٰنْ دُواْكِنْ يَاڧِ دَغَ مَصَرْ عَكَنْ أَظُرْڢَا طَرِے شِدَ دَ كُمَ دُواْكِ عَكَنْ أَظُرْڢَا طَرِے دَ حَمْسِنْ؞ تَهَكَنَنْ یَنْ كَاسُوَ نَسَرْكِے سُكَنْ شِغَرْدَ دَوَكِ دَ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْ يَاڧِ، سُسَاكٜىٰ سَيَرْ دَسُو غَ دُكَنْ سَرَاكُنَنْ هِتِّيَاوَا دَ سُرِيَاوَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Akan sayo karusa a Masar a bakin azurfa ɗari shida, doki kuwa a bakin ɗari da hamsin, 'yan kasuwar sarki sukan sayar da su ga dukan sarakunan Hittiyawa da na Suriyawa.