1 Kings 11:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A shekarun baya Dawuda ya ci Edom da yaƙi. Yowab, shugaban sojojinsa ya tafi can domin yă binne Isra’ilawa waɗanda suka mutu a yaƙi. Sa’ad da suke a can, sojojin Isra’ila suka kashe kowane ɗa namiji a Edom.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ شٜىٰكَرُنْ بَايَ دَاوُدَ يَثِ عٜىٰدُوامْ دَ يَاڧِ؞ أَ لُواْكَثِنْ كُوَ، يُواْوَبْ شُوغَبَنْ سُواْجُواْجِنْسَ يَتَڢِے وُرِنْ دُواْمِنْ يَبِنّٜىٰ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا وَطَنْدَ سُكَ مُتُ عَيَاڧِ؞ سَعَدَّ سُكٜىٰ أَوُرِنْ، سُواْجُواْجِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَ كَشٜىٰ كُواْوَنٜىٰ نَمِجِ أَ عٜىٰدُوامْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama sa'ad da Dawuda ya ci Edom, Yowab, shugaban sojoji, ya tafi don ya binne kisassu, sun yi wata shida a can, shi da mutanensa, sai ya kashe kowane namijin da yake cikin Edom.