1 Kings 11:25 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Rezon ya zama babban abokin gāban Isra’ila cikin dukan kwanakin mulkin Solomon. Ya ƙara rikici a kan rikicin Hadad. Rezon ya ƙi mulkin Isra’ila da dukan ransa. Saboda haka Rezon ya yi mulki a Aram ya kuma ƙi jinin Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
رٜىٰظُوانْ يَذَمَ بَبَّنْ أَبُواْكِنْ غَابَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ ثِكِنْ دُكَنْ ݣُونَكِنْ مُلْكٍ سُلَيْمَٰنُ؞ يَڧَارَ ضِكِثِ عَكَنْ ضِكِثِنْ هَدَدْ؞ رٜىٰظُوانْ يَڧِ مُلْكٍ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ دُكَنْ رَنْسَ، يَكُمَيِ مُلْكِ عَكَنْ سُورِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya zama abokin gāban Isra'ila a dukan zamanin Sulemanu. Ya yi ta ɓarna kamar yadda Hadad ya yi. Ya ƙi jinin mutane Isra'ila. Ya yi mulkin suriya.