1 Kings 11:26 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Haka ma Yerobowam, ɗan Nebat, shi ma ya yi wa sarki tawaye. Shi ɗaya ne daga shugabannin Solomon, shi mutumin Efraim ne daga Zereda, mahaifiyarsa kuwa gwauruwa ce, mai suna Zeruwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يٜىٰرُواْبُواْوَمْ طَنْ نٜىٰبَتْ، مُتُمِنْ إِڢْرَيِمْ دَغَ ظٜىٰرٜىٰدَ، طَيَ دَغَ ثِكِنْ دَتَّاوَا أَمُلْكٍ سُلَيْمَٰنُ، شِے مَا يَيِ وَ سَرْكِے سُلَيْمَٰنُ تَاوَيٜىٰ؞ سُونَنْ مَامَرْسَ ظٜىٰرُوَ وَدَّ مِجِنْتَ يَمُتُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Yerobowam ɗan Nebat, Ba'ifraime na Zaretan, baran Sulemanu, wanda sunan mahaifiyarsa Zeruya, wadda mijinta ya rasu, shi ma ya tayar wa sarki.