1 Kings 11:29 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da Yerobowam ya fita Urushalima, sai annabi Ahiya, mutumin Shilo ya tarar da shi a hanya. Lokacin kuwa Ahiya yana saye da sabuwar riga, ba kowa a filin sai su biyu kaɗai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَتَرَانَ يٜىٰرُواْبُواْوَمْ يَڢِتَ دَغَ عُرُوشَلِيمَ ذَاشِ وَنِ وُرِے، سَيْ يَغَمُ دَ أَنَّبِے أَهِيَ مُتُمِنْ شِلُواْ، سَنْيٜىٰ دَ سَابُوَرْ رِغَا؞ سُكَ غَمُ سُو بِيُ كَطَيْ عَكَنْ حَنْيَ بَايَنْ غَرِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A sa'ad da Yerobowam ya fita Urushalima, sai annabi Ahija mutumin Shilo ya tarar da shi a hanya. Lokacin kuwa Ahija yana saye da sabuwar riga, ba kowa a filin sai su biyu kaɗai,