1 Kings 12:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Matasan, waɗanda suka yi girma tare da shi, suka amsa, “Faɗa wa waɗannan mutanen da suka ce maka, ‘Mahaifinka ya sa kaya masu nauyi a kanmu, amma ka sassauta kayanka.’ Ka ce musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun tsohona kauri.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَمَارِنْ دَ سُكَيِ غِرْمَ تَرٜىٰدَ رٜىٰهُواْبُواْوَمْ سُكَثٜىٰ مَسَ «غَا أَمْسَرْ دَ ذَاكَبَا وَطَنْدَ سُكَثٜىٰ، ‹بَابَنْكَ يَسَا مَنَ غُنْ‌غُمٜىٰ وَنْدَ يَدَنّٜىٰمُ سُواْسَيْ، بَرِ كَيْ كَسَوْڧَڧَ مَنَ؞› كَأَمْسَ مُسُ كَثٜىٰ، ‹ڧَرَمَرْ يَڟَاتَ تَاڢِ ݣُونْݣُوسُوانْ بَابَنَ كَوْرِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Matasa da suke tsara ɗaya da shi kuwa suka ce masa, “Haka za ka faɗa wa mutanen nan da suka yi magana da kai, cewa tsohonka ya nawaita musu, amma sai ka sawwaƙa musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun tsohona kauri.