1 Kings 12:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka sarki bai saurare mutane ba, gama wannan abin da ya faru daga wurin Ubangiji ne, don a cika maganar Ubangiji da ya yi wa Yerobowam ɗan Nebat ta wurin Ahiya, mutumin Shilo.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے بَيْ سَوْرَرِ جَمَعَرْبَ؞ غَمَا نُڢِنْ يَهْوٜىٰهْ نٜىٰ دُواْمِنْ يَكَٰوُاْ ثِكَرْ مَغَنَرْسَ دَ يَيِ غَ يٜىٰرُواْبُواْوَمْ طَنْ نٜىٰبَتْ تَبَاكِنْ أَنَّبِے أَهِيَ مُتُمِنْ شِلُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haka kuwa sarki ya ƙi jin roƙon da jama'a suka yi masa, gama Ubangiji ne ya sa al'amarin ya zama haka domin ya cika maganarsa, wadda ya yi wa Yerobowam ɗan Nebat ta bakin Ahija mutumin Shilo.