1 Kings 12:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
‘Ga abin da Ubangiji ya ce, “Kada ku haura don ku yi yaƙi da ’yan’uwanku, Isra’ilawa. Ku koma gida, kowannenku, gama wannan aikina ne.” ’ ” Saboda haka suka yi biyayya da maganar Ubangiji, suka sāke watse zuwa gida, yadda Ubangiji ya umarta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
‹إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ «كَدَ كُڢَاطَ وَیَنْعُوَنْكُ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا دَ يَاڧِ؞ بَرِ كُواْوَنٜىٰ مُتُمْ يَكُواْمَ غِدَنْسَ، غَمَا وَنَّنْ أَبُ دَغَ وُرِينَ نٜىٰ؞» › » سَيْ سُكَيِ بِيَيَّ دَ مَغَنَرْ يَهْوٜىٰهْ ، سُكَ كُواْمَ غِدَاجٜىٰنْسُ بِسَغَ عُمَرْنِنْ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya ce, “Kada ku haura zuwa yaƙi da 'yan'uwanku, mutanen Isra'ila, sai kowa ya koma gidansa, gama wannan al'amari daga wurina ne.” Su kuwa suka yi biyayya da maganar Ubangiji, suka koma gida.