1 Kings 12:32 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya kafa biki a rana ta goma sha biyar ta watan takwas, kamar bikin da ake yi a Yahuda, ya kuma miƙa hadayu a bisa bagade. Ya yi haka a Betel, yana miƙa wa siffofin maruƙan da ya yi hadayu. A Betel kuma ya naɗa firistoci a wuraren tudun da ya yi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يٜىٰرُواْبُواْوَمْ يَكُمَ كَڢَ بِكٍ أَدِّينِ أَ رَانَ تَغُواْمَشَا بِيَرْ نَوَتَنْ تَݣُوسْ دَيْدَيْ كَمَرْ بِكٍ أَدِّينِنْ دَ عَكٜىٰيِ أَ يَهُودَ؞ عَكَنْ بَغَدٜىٰنْ دَيَكٜىٰ أَ بٜىٰتٜىٰلْ، يٜىٰرُواْبُواْوَمْ يَمِيڧَ هَدَايُ غَ صِڢُّواْڢِنْ یَنْ بِجِمَيْ نَظِينَارِيَرْ نَنْ دَ يَيِ؞ أَ بٜىٰتٜىٰلْ كُمَ يَنَطَ ڢِرِسْتُواْثِے نَوَطَنْسُ وُرَارٜىٰنْ سُجَّدَ، وَطَنْدَ يَغِغِّنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yerobowam kuma ya sa a yi idi ran goma sha biyar ga wata na takwas kamar yadda ake yi a Yahuza. Ya miƙa hadayu bisa bagade, haka ya yi a Betel. Ya yi ta miƙa hadayu ga siffofin maruƙan da ya yi. Ya kuma sa firistoci a masujadan da ya gina a Betel.