1 Kings 13:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yayinda yake kan hanyarsa, sai wani zaki ya sadu da shi ya kashe shi, aka kuma jefar da jikinsa a kan hanya, jakin da zakin suka tsaya kusa da gawar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ مُتُمِنْ اللَّهْ يَكٜىٰ تَڢِيَ سَيْ وَنِ ذَاكِ يَغَمُ دَشِ عَكَنْ حَنْيَ يَكَشٜىٰشِ؞ جِكِنْسَ كُوَ يَنَ ݣُونْثٜىٰ عَڧَسَا، جَاكِنْ يَنَ ڟَيٜىٰ كُسَدَشِ أَوُرِنْ؞ ذَاكِنْ شِے مَا يَنَ ڟَيٜىٰ كُسَدَ جِكِنْ مُتُمِنْ اللَّهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da annabin Allah ya tafi, sai zaki ya gamu da shi a hanya, ya kashe shi, ya jefar da gawarsa a kan hanya. Sai jakin da zakin suka tsaya kusa da gawar.