1 Kings 13:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A wannan rana mutumin Allah ya ba da alama, “Ga alamar da Ubangiji ya furta. Wannan bagade zai tsage yă rabu kashi biyu, tokar da yake a kansa za tă zuba a ƙasa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ رَانَرْ نَنْ سَيْ يَبَادَ عَلَمَ يَثٜىٰ «غَا عَلَمَرْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَبَايَرْ؞ وَنَّنْ بَغَدٜىٰ ذَيْ ڟَٰغٜىٰ يَرُشٜىٰ، تُواْكَرْ دَتَكٜىٰ عَكَنْسَ ذَاتَ ظُبَ ڧَسَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya kuma ba da alama a wannan rana cewa, “Wannan ita ce alamar da Ubangiji ya faɗa, za a rushe bagaden, a zubar da tokar da take bisansa.”