1 Kings 13:33 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Har ma bayan wannan, Yerobowam bai canja daga mugayen hanyoyinsa ba, amma ya ƙara naɗa firistoci domin masujadai da suke kan tuddai daga kowane irin mutane. Duk wanda ya so yă zama firist sai yă naɗa shi don aiki a masujadai da suke kan tuddai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ وَطَنَّنْ أَبُبُوَ، يٜىٰرُواْبُواْوَمْ بَيْ بَرْ مُوغُوَرْ حَنْيَرْسَبَ؞ يَسَاكٜىٰ نَطَ ڢِرِسْتُواْثِے بَرْكَتَيْ دَغَ ثِكِنْ دُكَنْ مُتَنٜىٰ؞ دُكْ وَنْدَ يَسُواْ ذَمَنْ ڢِرِسْتِ يَكَنْ نَطَشِ دُواْمِنْ سُيِ عَيْكِ أَوَطَنْسُ وُرَارٜىٰنْ سُجَّدَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan wannan al'amari Yerobowam bai bar muguwar hanyarsa ba, amma ya naɗa firistoci daga cikin mutane don masujadai da suke kan tuddai. Duk mutumin da yake so, sai ya keɓe shi don ya zama firist na masujada da take kan tudu.