1 Kings 13:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da Yerobowam ya ji abin da mutumin Allah ya tā da murya ya faɗa game da bagaden Betel, sai ya miƙa hannunsa daga bagaden ya ce, “Ku kama shi!” Amma sai hannun da ya miƙa ya yanƙwane, har bai iya janye shi ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ سَرْكِے يَجِ أَنَّبْثِنْ مُتُمِنْ اللَّهْ نَّنْ نَغَابَادَ بَغَدٜىٰنْ بٜىٰتٜىٰلْ، سَيْ سَرْكِے يٜىٰرُواْبُواْوَمْ يَمِيڧَ حَنُّ يَنَ ثٜىٰوَ «كُكَامَشِ!» عَمَّا حَنُّنْدَ يَمِيڧَ مَسَ يَشَنْيٜىٰ، بَيْ عِيَ جَنْيٜىٰشِيبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da sarki ya ji maganar annabin, wato wadda ya yi a kan bagaden da yake Betel, sai ya miƙa hannunsa daga bagaden, ya ce, “Ku kama shi.” Hannun da ya miƙa kuwa ya sage, bai iya komo da shi ba.