1 Kings 14:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Saboda wannan, zan kawo masifa a gidan Yerobowam. Zan yanke kowane ɗa na ƙarshe a Isra’ila, bawa ko ’yantacce. Zan ƙone gidan Yerobowam kamar yadda mutum yakan ƙone juji, sai duk ya ƙone ƙurmus.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ، غَاشِ، ذَنْ كَٰوُاْ مَسِيڢَ عَكَنْ غِدَنْكَ؞ ذَنْ كَوَرْدَ دُكَنْ یَیَنْكَ مَظَا، كُواْ سُو بَايِ نٜىٰ، كُواْ سُو بَ بَايِ بَنٜىٰ عَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ ذَنْ كُمَ ثِنْيٜىٰ ذُرِيَرْكَ كَمَرْ يَدَّ مُتُمْ يَكَنْ ڧُواْنٜىٰ تَاكِنْ دَبُّواْبِے حَرْ سَيْ يَڧَارٜىٰ ڧُرْمُسْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saboda haka zan kawo masifa a gidanka. Zan datse maka kowane ɗa namiji, ko bawa, ko 'yantacce, daga cikin Isra'ila. Zan ƙone gidanka kamar yadda akan ƙone juji ƙurmus.