1 Kings 14:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yahuda ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Ta wurin zunuban da suka yi, sun tā da fushin kishinsa fiye da yadda kakanninsu suka yi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ يَهُودَ كُوَ سُكَ عَيْكَتَ مُغُنْتَا أَعِدُوانْ يَهْوٜىٰهْ ڢِيٜىٰدَ يَدَّ كَاكَنِّنْسُ سُكَيِ؞ يَوَنْ ذُنُبَنْسُ يَڟُواْكَنٜىٰ يَهْوٜىٰهْ يَيِ ڢُشِے سُواْسَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutanen Yahuza suka yi wa Ubangiji zunubi. Suka tsokane shi ya yi fushi saboda zunuban da suka aikata fiye da abin da kakanninsu suka yi.