1 Kings 15:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura, ya yi yaƙi da Yahuda, ya kuma gina Rama don yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa, sarkin Yahuda.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَرْكِے بَعَشَ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ يَكَيْوَ يَهُودَ يَاڧِ؞ يَكُمَ ڠَغْڠَرَ رَمَ دُواْمِنْ يَحَنَ كُواْوَ ڢِتَ دَ شِغَ وُرِنْ سَرْكِے أَسَ نَ يَهُودَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba'asha, Sarkin Isra'ila, ya kai wa Yahuza yaƙi. Sai ya gina Rama don ya hana kowa ya fita ko kuma ya shiga wurin Asa, Sarkin Yahuza.