1 Kings 15:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Asa ya ɗauki dukan azurfa da kuma zinariyar da suka rage a ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma nasa fadan, ya ba da su ga wani shugabansa, ya kuma aika da su zuwa ga Ben-Hadad ɗan Tabrimmon, ɗan Heziyon, sarkin Aram, wanda yake mulki a Damaskus.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ أَسَ يَطَوْكِ دُكَنْ أَظُرْڢَا دَ ظِينَارِيَرْ دَسُكَ رَغُ ثِكِنْ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ دَ ثِكِنْ غِدَنْ سَرْكِے، يَدَنْڧَ أَ حَنُّنْ دَتَّاوَنْسَ سُكَيْ وَ سَرْكِے بٜىٰنْهَدَدْ نَ سُورِيَ وَنْدَ يَكٜىٰ ذَمَ أَ دِمَشْڧُ؞ بٜىٰنْهَدَدْ طَنْ تَبْرِمُّوانْ نٜىٰ، جِيكَنْ هٜىٰظِيُوانْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Asa ya kwashe dukan azurfa da zinariya da suka ragu a ɗakunan ajiya na Haikalin Ubangiji, da na gidan sarki, ya ba barorinsa su kai wa Ben-hadad ɗan Tabrimmon, ɗan Heziyon, Sarkin Suriya, wanda yake zaune a Dimashƙu, ya ce,