1 Kings 15:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakanina da kai, kamar yadda ta kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Duba, ina aika maka kyautai na azurfa da na zinariya. Yanzu fa sai ka janye yarjejjeniyarka da Ba’asha sarkin Isra’ila, don yă janye daga gare ni.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَسَ يَثٜىٰ مَسَ «بَرِ مُسَابُنْتَ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَرْمُ ڟَكَانِنْ بَابَنْكَ دَ بَابَنَ؞ غَا أَظُرْڢَا دَ ظِينَارِيَ نَعَيْكُواْ مَكَ دُواْمِنْ كَكَرْيَ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ دَ سَرْكِے بَعَشَ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ دُواْمِنْ يَجَنْيٜىٰ دَغَ ڧَسَاتَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Bari mu ƙulla alkawari da juna kamar yadda tsohona da tsohonka suka yi, ga shi, na aika maka da kyautar azurfa da zinariya. Sai ka tafi, ka warware alkawarinka da Ba'asha, Sarkin Isra'ila, domin ya tashi ya bar ni.”