1 Kings 15:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ben-Hadad ya yarda da maganar Sarki Asa, ya kuma aika shugabannin sojojin mayaƙansa ya yi yaƙi da garuruwan Isra’ila. Ya kame Iyon, Dan, Abel-Bet-Ma’aka da dukan Kinneret, haɗe da Naftali.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے بٜىٰنْهَدَدْ يَيَرْدَ دَ مَغَنَرْ أَسَ؞ سَيْ يَعَيْكَ دَ شُوغَبَنِّنْ سُواْجُواْجِنْسَ تَرٜىٰدَ سَوْرَنْ سُواْجُواْجِنْ سُكَيْ يَاڧِ عَكَنْ بِرَنٜىٰنْ ڧَسَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ سُكَ ڨُوثٜىٰ غَرُضُوً إِيُوانْ دَ دَنْ دَ أَبٜىٰلْ بٜىٰتْ مَعَكَ دَ وُرِنْ دَيَكٜىٰ كُسَدَ تَڢْكِنْ غَلِيلِ دَ دُكَنْ يَنْكِنْ نَڢْتَلِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ben-hadad kuwa ya yarda da maganar sarki Asa. Ya kuwa aiki shugabannin sojojinsa su yi yaƙi da garuruwan Isra'ila. Su kuwa suka tafi, suka ci Iyon, da Dan, da Abel-bet-ma'aka, da dukan Kinneret, da dukan ƙasar Naftali.