1 Kings 15:29 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Nan da nan da ya fara mulki, sai ya kashe dukan iyalin Yerobowam. Bai bar wa Yerobowam wani da rai ba, amma ya hallaka su duka, bisa ga maganar Ubangiji da ya ba wa bawansa Ahiya, mutumin Shilo.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ يَذَمَ سَرْكِے سَيْ نَنْ دَنَنْ يَكَشٜىٰ دُكَنْ غِدَنْ يٜىٰرُواْبُواْوَمْ؞ بَيْ بَرْ كُواْ مُتُمْ طَيَ دَ رَيْ بَ، يَهَلَكَاسُ كَكَڢْ، بِسَغَ مَغَنَرْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَيِ تَبَاكِنْ بَاوَنْسَ أَنَّبِے أَهِيَ مُتُمِنْ شِلُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Nan da nan da ya zama sarki, sai ya kashe dukan mutanen gidan Yerobowam, bai bar wani na gidan Yerobowam da rai ba, ya hallaka su sarai, bisa ga maganar Ubangiji wadda ya faɗa wa bawansa Ahija mutumin Shilo.