1 Kings 16:29 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A shekara ta talatin da takwas ta Asa sarkin Yahuda, Ahab ɗan Omri ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki a Samariya a kan Isra’ila, shekara ashirin da biyu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ شٜىٰكَرَا تَتَلَتِنْ دَ تَݣُوسْ تَمُلْكٍ سَرْكِے أَسَ نَ يَهُودَ، أَهَبْ طَنْ عُوامْرِ يَڢَارَ مُلْكٍ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ أَهَبْ يَيِ مُلْكِ أَ سَمَرِيَ شٜىٰكَرَا عَشِرِنْ دَبِيُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A shekara ta talatin da takwas ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ahab ɗan Omri ya yi sarautar Isra'ila. Ahab ɗan Omri kuwa ya yi sarautar Isra'ila a Samariya shekara ashirin da biyu.