1 Kings 16:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ban da haka, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Yehu ɗan Hanani wa Ba’asha da gidansa, saboda dukan muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, ya tsokane shi yă yi fushi ta wurin abubuwan da ya yi, da kuma zama kamar gidan Yerobowam, da kuma domin ya hallaka gidan Yerobowam.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنَّنْ مَغَنَرْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَڢَطَا نٜىٰ تَبَاكِنْ أَنَّبِے يٜىٰهُو طَنْ هَنَنِ عَكَنْ بَعَشَ دَ غِدَنْسَ؞ تَا ذُواْ نٜىٰ سَبُواْدَ دُكَنْ مُغُنْتَارْدَ يَعَيْكَتَ أَعِدُوانْ يَهْوٜىٰهْ ؞ بَعَشَ يَسَا يَهْوٜىٰهْ يَيِ ڢُشِے سَبُواْدَ أَيُّكَنْ حَنُّوَنْسَ دَ يَعَيْكَتَ دَيْدَيْ كَمَرْ نَغِدَنْ يٜىٰرُواْبُواْوَمْ دَ كُمَ سَبُواْدَ يَكَشٜىٰ عِيَلِنْ يٜىٰرُواْبُواْوَمْ غَبَاطَيَ؞ ﴿شٜىٰكَرَا 886-885 كَاڢِنْ حَيْڢُوَرْ عِيسَىٰ ﴾
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji kuma ya yi magana da Yehu ɗan Hanani, a kan Ba'asha da gidansa, saboda muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, har ya sa Ubangiji ya yi fushi, gama abin da ya aikata ya yi daidai da na Yerobowam, saboda kuma ya hallaka gidan Yerobowam.