1 Kings 16:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zimri, ɗaya daga cikin shugabanni, wanda ya shugabanci rabin kekunan yaƙin Ela, ya yi maƙarƙashiya a kansa. Ela yana a Tirza a lokacin, ya bugu a gidan Arza, sarkin fada a Tirza.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا ظِمْرِ، طَيَ دَغَ ثِكِنْ شُوغَبَنِّنْ سُواْجُواْجِنْ وَنْدَ يَكٜىٰ لُورَ دَ رَبِنْ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْ يَاڧِنْسَ، يَيِ ڧُلّٜىٰ ڧُلّٜىٰنْ كَشٜىٰشِ؞ سَعَدَّ عٜىٰلَ يَكٜىٰ أَ تِرْظَ أَغِدَنْ أَرْظَ شُوغَبَنْ غِدَنْ سَرْكِے، يَشَا يَبُغُ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma Zimri, shugaban rabin karusan Ila, ya yi masa maƙarƙashiya. Sa'ad da Ila yake Tirza, ya sha, ya bugu a gidan Arza wanda yake lura da fāda,