1 Kings 17:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Iliya ya ce, “Ki miƙa mini ɗanki.” Sai ya ɗauke shi daga hannuwanta, ya kai shi ɗakin sama inda yake zama, ya kwantar da shi a gadonsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِلْيَاسُ يَثٜىٰ «كِمِيڧُواْ مِنِ يَرُوانْكِ؞» يَكَرْٻِ يَرُوانْ دَغَ حَنُّنْتَ يَهَوْرَ دَشِ طَاكِنْ سَمَ عِنْدَ يَكٜىٰ ذَمَ، يَݣُونْتَرْدَ يَرُوانْ أَغَدُوانْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Iliya ya ce mata, “Ki kawo mini ɗanki.” Ya karɓe shi daga wurinta, ya kai shi a bene inda yake kwana. Ya kwantar da shi a gadonsa.