1 Kings 17:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka sai Iliya ya yi abin da Ubangiji ya faɗa masa. Ya tafi Rafin Kerit, gabas da Urdun, ya zauna a can.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِلْيَاسُ كُوَ يَتَڢِے بِسَغَ مَغَنَرْ يَهْوٜىٰهْ ، يَتَڢِے يَذَوْنَ أَوَجٜىٰنْ رَاڢِنْ كٜىٰرِتْ وَنْدَ يَكٜىٰ غَبَسْ دَ كُواْغِنْ يُواْدَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Iliya kuwa ya tafi, ya yi yadda Ubangiji ya faɗa, ya tafi ya zauna a rafin Kerit wanda yake gabashin Urdun.