1 Kings 18:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yanzu ka tara mutane daga dukan Isra’ila su sadu da ni a kan Dutsen Karmel. Ka kuma kawo annabawa ɗari huɗu da hamsin na Ba’al, da kuma annabawa ɗari huɗu na Ashera, waɗanda suke ci a teburin Yezebel.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ، كَعَيْكَ عَتَتَّارَ دُكَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ ذُوَا بَبَّنْ تُدُنْ كَرْمٜىٰلْ، تَرٜىٰدَ أَنَّبَاوَا طَرِے حُطُ دَ حَمْسِنْ نَ بَعَلْ دَ أَنَّبَاوَا طَرِے حُطُ نَ أَشٜىٰرَ، وَطَنْدَ سُكٜىٰ ثِنْ عَبِنْثِ أَ حَنُّنْ يٜىٰظٜىٰبٜىٰلْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yanzu fa ka aika a tattara mini Isra'ila duka a dutsen Karmel, da annabawan Ba'al, su ɗari huɗu da hamsin, da annabawan Ashtarot kuma, su ɗari huɗu waɗanda Yezebel take kula da su.”