1 Kings 18:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ku samo mana bijimai biyu. Bari su zaɓa ɗaya wa kansu, bari kuma su yanka shi kucu-kucu su sa a itace, sai dai, kada su sa wuta a kansa. Ni kuwa zan shirya ɗaya bijimin in sa a kan itace, ni ma, ba zan sa wuta a kansa ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عَبَامُ بِجِمَيْ بِيُ؞ بَرِ سُذَاٻَا وَكَنْسُ بِجِمِ طَيَ، سُيَيَّنْكَ شِ، سُشِمْڢِطَا عَكَنْ إِتَاثٜىٰ، عَمَّا كَدَ سُكُنَّ وُتَا عَكَنْسَ؞ نِے كُمَ ذَنْ طَوْكِ بِجِمِ طَيَ إِنْشِرْيَ شِ عَكَنْ إِتَاثٜىٰنْ، بَذَنْ كُمَسَا مَسَ وُتَا بَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
To, a ba mu bijimi biyu, su su zaɓi guda su yanyanka gunduwa gunduwa, su shimfiɗa a kan itacen wuta, amma kada su kunna masa wuta. Ni kuma zan shirya ɗaya bijimin, in shimfiɗa bisa itacen wuta ba kuwa zan kunna masa wuta ba.