1 Kings 18:27 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da tsakar rana, Iliya ya fara yin musu ba’a. Ya ce, “Ku yi ihu da ƙarfi, tabbatacce shi allah ne! Mai yiwuwa yana cikin zurfin tunani, ko dai aiki ya yi masa yawa, ko ya yi tafiya. Mai yiwuwa yana barci ne, dole a tashe shi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ ڟَكَرْ رَانَ تَيِ، سَيْ إِلْيَاسُ يَيِمُسُ غُواْرِ يَثٜىٰ «كُيِ كِرَا دَ بَبَّرْ مُرْيَ، أَيْ، شِے اللَّهْ نٜىٰ! وَتَڧِيلَ يَنَ تُنَانِ، كُواْ كُوَ يَڢِتَ يَٰوُاْ نٜىٰ، كُواْ كُوَ يَيِ تَڢِيَ؞ وَتَڧِيلَ كُمَ يَنَ بَرْثِ نٜىٰ، سَيْ عَتَاشٜىٰشِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da rana ta yi tsaka sai Iliya ya yi musu ba'a, ya ce musu, “Ku kira da babbar murya, gama shi wani allah ne, watakila yana tunani ne, ko kuwa ya zagaya ne, ko kuma ya yi tafiya. Watakila kuma yana barci ne, sai a tashe shi.”