1 Kings 18:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yayinda Yezebel tana kisan annabawan Ubangiji, Obadiya ya ɗauki annabawa ɗari ya ɓoye a kogwanni biyu, hamsin a kowanne, ya kuma tanada musu abinci da kuma ruwa.)
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ لُواْكَثِنْ دَ يٜىٰظٜىٰبٜىٰلْ تَكٜىٰ كَشٜىٰ أَنَّبَاوَنْ يَهْوٜىٰهْ كُوَ، سَيْ عُواْبَدِيَ يَٻُواْيٜىٰ أَنَّبَاوَا طَرِے عَكُواْغُواْ بِيُ، حَمْسِنْ عَكُواْوَنٜىٰ كُواْغُواْ؞ يَنَ كُمَبَاسُ عَبِنْثِ دَ ضُوً شَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Ubangiji, Obadiya ya kwashe annabawa ɗari ya raba su hamsin hamsin ya ɓoye su a kogo, ya ciyar da su, ya shayar da su.